Rikita-Rikita! Kowa yayi ta kansa, zaki 4 sun tsere daga gandun daji
- Kowa yayi ta kansa, zaki 4 sun tsere daga gandun daji
- Zakuna 4 sun tsere ne a kasar Afrika ta kudu
- Sun dai tsere ne tun ranar Lahadi
Mahukunta a kan kasar Afrika ta kudu na can sun dukufa ka'in da na'in wajen kokarin gano wasu zakuna hudu da suka tsre daga gandun dajin kasar.
Mahukuntan sunce zakunan kosassu ne kuma sun gudu ne tun ranar Lahadin da ta gabata sannan kumar har inda yau take ba'a gansu ba kuma ba'aji labarin su.
Legit.ng ta samu labarin cewa daga nan ne fa sai mahukuntan na kasar suka shawarci mutanen kasar musamman ma masu makwaftaka da dajin da suyi taka tsantsan.
Hakan dai na zuwa ne bayan da a cikin watan Mayu wasu zakokin guda biyar suka tsere daga wannan gandun daji.
Amma daga bisani an sake cafke hudu, sai dai har yanzu na biyar din babu labarinsa.
Asali: Legit.ng