Ku noma doya-Audu Ogbe ya maida martani ga masu sukan sa akan fitar da doya kasan waje

Ku noma doya-Audu Ogbe ya maida martani ga masu sukan sa akan fitar da doya kasan waje

-Ministan harkan noma ya mai da martini ga masu sukan sa, kuma yace babu karanci doya a kasan

-Ministan yace fitar da doya kasan waje zai gyara tattalin arzikin kasan

-Yayi kira da yan Nigeria da su rage yin suka da duk wani kudiri da gwmanti a kawo dan ci gaban al umma

Ku noma doya-Audo Ogbe ya maida martani ga masu sukan sa akan fitar da doya kasan waje.
Audu Ogebe ministan harkan noma da raya karkara.

Audu Ogbe ministan harkan noma da raya karkara yayi kira da masu sukan sa akan kuduri da gwmnati keyi dan fitar da doya waje. Da suma su yi irin na su noman.

Yayin da yak e Magana da yan jarida a Abuja 10 ga watan yuli yayi watsi masu sukan kudirin. Yace kudirin zai kawo cigaba sosai ma tattalin arzikin kasan.

KU KARANTA:h Shaye-shaye cikin yan matan arewa ya zama ruwan dare - SultanYa ce karfin da yan adawa ke sawa a wajen suka kudurin da sun sashi a wajen aikin noma doya. saboda Shuka ne da ke fitowa a kowani sashen kasan.

Minister yayi ma wa yanda suke tunani kudirin zai janyo karancin doya a fadin kasan. Cewa yanzu haka akwai karanci manoman doya saboda haka kudirin zai janyo yawan doya.

Jama’aa na ta suka cewa akwai karanci doya a kasan koma gwamanti na kokarin fitar da doya, kuma yan kasa na cikin yunwa

Yace kashi 30% na da doya da ake nomawa yana lalacewa saboda rashin kimiyan ajiya.

Kasar Ghana ce kan gaba wajen fitar da doya kasashen waje kuma mafi akasarin doyan da suke fitarwa daga kasannan ne.

Yakara cewa ba ‘a taba samu karancin doya a kasannnan ba.

“Mai yasa ku ke tunani haka? Mai yasa kuke ja da baya wajen gwada sabon abu saboda son zuciya” ministan ya tabaya.

“ Masana sun a cewa ya kamata mu kara ma doya daraja saboda mu samu kudade masu yawa.

“ Sun manta da cewa kilo 3 na doya ya kai $15, a kudin ngeria ya kai N5,000.

“ A Kasar Landon doya 3 kachal ke cikin carton a 30 pounds.

“a wannan farashin kasan za tafi samun kudin da zai daga darajar tattalin arzikin ta."

Ministan ya yabi kungiyan standard organization of Nigeria(SON) na tsara kaidoji masu kyau da za abi wajen fitar da doya waje. Yayi alkwari da za ayi kokari bin kaidoin.

Mr Audu Ogbe yayi kira da kwamishinonin jahihi da su jajirce wajen illimantar da manoma wajen amfani da Iri ma kyau wajen noma doya. Saboda samun amfani gona mai yawa.

An kadammar da kudirin fitar da doya a Nigreia kasan waje a ranar 29 watan juli a Lillypond container terminal Lagos wanda ministan noma Audu Ogbe ya kaddmar da kanshi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel