Siyasa: Nasarar PDP a zaben jihar Osun alamar karshen APC a Najeriya - Inji 'yan majalisar PDP

Siyasa: Nasarar PDP a zaben jihar Osun alamar karshen APC a Najeriya - Inji 'yan majalisar PDP

- ‘Yan majalisar PDP sun nuna farin cikinsu ga nasarar da jam’iyyar ta samu a zabe jihar Osun

- Honarabul Leo Ogor ya ce wannan shine farkon karshen jam’iyyar mai mulki APC a kasar

- Dan takarar PDP ya kada abokin gabansa Mudashiru Hussein na APC da kuri’u 97, 280

‘Yan jam'iyyar PDP a Majalisar Wakilan Najeriya sun bayyana nasarar da dan takarar jami’iyyar ya samu a zaben sanata da aka kammala a mazabar jihar Osun ta yamma a matsayin wata alamar kawo karshen jama'iyyar mai mulki ta APC.

A wata sanarwar shugaban 'yan tsiraru, Leo Ogor ya taya dan takarar jam’iyyar PDP Ademola Adeleke da ‘yan jam’iyyar PDP a jihar da kuma mutanen Jihar Osun baki daya murnar nasara da jam’iyyar ta samu.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Mista Adeleke dan takarar PDP ya lashe kananan hukumomi 10 daga cikin 11 a mazabar jihar Osun ta yamma inda ya kada abokin gabansa, Mudashiru Hussein da kuri’u 97, 280.

Nasarar PDP a zaben jihar Osun farkon karshen jam’iyyar APC a Najeriya - Inji 'yan majalisar PDP
Shugaban 'yan tsiraru a majalisar wakilai, Leo Ogor; Tushen hoto: Facebook, Rt. Hon Leo Okuweh Ogor

KU KARANTA: Idan aka ba Matasa dama za su gyara Najeriya - Attahiru Jega

“Lalle, rashin ayyukan yi da tsaro da kuma rashin magance kashe kashe na makiyaya a fadin kasar ba tare da wani hukunci ba, wadannan abubuwan zasu kayyade makomar jam’iyyar APC a zaben shekarar 2019”. Inji ‘yan majalisar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel