Matsalar shaye-shaye tsakanin matan arewa ta ta'azzara
- Matsalar shaye-shayen mata a arewa ta ta'azzara
- Yanzu dai matan aure, yan mata da zawarawa sun fi yin shaye-shayen
- An bukaci mutane su sa ido wajen tarbiyyar 'yayan su
Matsalar shaye-share da kuma tu'ammali da kayan maye a tsakanin matan arewacin kasar nan na kara kamari a cikin al'umma.
Wannan dai yana daya daga cikin batutuwan da hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi watau NDLEA ta ke yaki da su ka'in da na'in yanzu haka.
Hukumar ta bayyana cewa yanzu haka dai matan aure da yan mata tare kuma da zawarawa sune kan gaba a wajen harka da kwayoyin.
Legit.ng ta samu cewa Alhaji Hamza Umar babban kwamandan hukumar da ke yaki da shan miyagu kwayoyi na jihar Kano ya ce abin ya yi matukar yawa a jihar Kano, wanda matsalar ta fi yawa a tsakanin matan aure, da zawarawa, da kananan 'yanmata, da ko biki ake sai sun tanade su.
Asali: Legit.ng