Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

- Kamfanonin suminti zasu rage farashin sa

- Masu ruwa da tsaki na harkar ta suminti sun gana da Osinbajo

- Gwamnati zata taimakawa masu sana'ar ta siminti

Gamayyar kamfunnan suminti da kuma manyan yan kasuwa dillallan sa sun sanar da cewa nan ba da dadewa ba zasu karyar da kudin sumintin a kasuwa.

Mun samu labari daga majiyar mu cewa shugaban kamfanin da ke yin sumintin nan na BUA watau Alhaji Abdussamad Isyaka rabi'u shine ya bayyana hakana wata fira da yayi da yan jarida lokaci kadan bayan sun gama ganawa da mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria
Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

Legit.ng ta samu labarin cewa Shugaban na kamfanin BUA ta ta'allaka tsadar da sumintin yayi da rashin imani na wasu yan kasauwa sannan kuma da karancin wani muhimmin sinadarin da ake anfanin da shi wajen yin sumintin na LPFO a turance.

Sai ya kara da cewa: "Amma yanzu gwamnati a zaman da tayi da mu ta tabbatar mana da cewa dukkan wannan matsalolin zasu kaura don haka suma mutane su shirya samun sumintin cikin sauki."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng