Anyi gangamin fara yi ma ɗan majalisa Abdulmuminu Jibrin kiranye a garin Dakatsalle

Anyi gangamin fara yi ma ɗan majalisa Abdulmuminu Jibrin kiranye a garin Dakatsalle

- Jama'an kasar nan sun fara wayewa da yi ma yan majalisunsu kiranye

- Yan mazabar Abdulmuminu Jibrin Kofa sun fara shirya masa kiranye

Daruruwan jama’a daga mazaɓar Ƙiru da Bebeji sun fara gangamin yi ma dan majalisar su Abdulmuminu Jibrin kiranye daga majalisar wakilai ta tarayya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan taro ya gudana ne a garin Dakatsalle, inda shugaban gangamin ALhaji Salele Bushasha ya bayyana cewar sun kudirci yi ma Jibrin kiranye ne saboda rashin girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

“Abdulmuminu Kofa baya nuna damuwa ga al’ummarsa, kuma baya girmama shuwagabannin majalisar wakilai, don haka ne muka tattara dukkanin bayanan da suka dace don yi masa kiranye, zamu fara wannan yunkuri a ranar 30 ga watan Yuli”

Anyi gangamin fara yi ma ɗan majalisa Abdulmuminu Jibrin kiranye a garin Dakatsalle
Abdulmuminu Jibrin

Bushasha ya kara da cewa tunda dai Jibrin yayi watsi dasu, toh zai gani a kwaryarsa, don haka zasu dawo da shi gida, inji majiyar Legit.ng.

Cikin wadanda suka halarci gangamin akwai shugaban kungiyar Matasa reshen karamar hukumar Bebeji, Abdulrashid Isah, shugaban kungiyar Malamai, NUT reshen Bebeji, Yusf Garba da suaran yan siyasa daga manyan jam’iyyun adawa da APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin yan Najeriya sun gaji da mulkin Buhari ne?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng