Yadda na ku sa rasa rayuwata
- Mazaunin Ikorodu ya bayyana yadda ya kusa rasa ranshi
- Wasu mutane sunyi zargin wannan mutum dan kungiyar shan jini ne
- Mazaunin dai yace yanzu hadari ne fitowa bayan karfe 7 na dare
Wani mutum mazaunin Ikorodu ta Jihar Legas me suna Akinrinlade Ayodeji ya tsallake rijiya da baya a sakamakon zargin shi da wasu mazauna yankin suka yi ma sad a cewa shi dan kungiyar shan jini ne wanda wasu kan ce ‘yan mafiya.
Ayodeji dai ya ba da labarin yadda ya kusa rasa ranshi bisa ga zaton da mazauna yankin suka yi mishi a shafin facebook. Ya rubuto cewa wannan abu dai ya zama rowan dare sakamakon hakan ba a kanshi kadai ta taba faruwa ba.
Ya ruboto cewa a lokacin da yake kan hanyar shi ta zuwa debo ruwa domin amfanin gidanshi, da misalin karfe 7:39 na dare. Sai kawai wasu mutane suka far masa , yana kokarin ya bayyana musu ko shi waye da kuma abinda ya fito das hi, amma ka fin ya ankara sunyi masa jina-jina domin abun dake faruwa a yankin yana ci musu tuwo a kwarya.
Sai daga bisani suka gano cewa ai wannan mutum dai na gari ne ba ire-iren wanda suke zargi bane bayan da mutanen gari su ka kawo masa dauki, sannan suka nemi shi da yafe musu.
Ayodeji dai yace wannan abun dai ba kanshi farau ba, domin kuwa hakan har akan wani abokin su ta faru, sai dai shi abokin bai tsawon rai ba da zai ba da labara ba, domin kuwa shi har lahira suka aika shi.
KU KARANTA: Teku na kokarin hadiye jihar Legas, duba hotunan ambaliyar
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas Olarinde Famous yayi korafi akan ire-iren faruwar wannan abubuwa a yankin, kuma yace hakan yana faruwa ne sanadiyar kama wasu ‘yan kungiyar da rundunar ta ‘yan sanda take yi a yankin Ikorodu na Jihar Legas.
Famous ya sha alawashin cewa zasu yi iya ka cin bakin kokarin su domin su ga cewa sun kame duk wani dan kungiyar ta shan jini ba ma a iya yankin kadai ba har Jihar tasu baki daya.
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng