Za'a yi ganawa tsakanin Rahama Sadau da Priyanka Chopra ta Indiya

Za'a yi ganawa tsakanin Rahama Sadau da Priyanka Chopra ta Indiya

- Rahama Sadau zata yi ganawa da Priyanka Chopra kan wasu batutuwa

- Ta shaidawa manema labarai cewa dama can suna magana

- Ta ce wannan karon ganawarsu ta daban ce

Rahama Sadau, jaruma da ke son tayi fina-finan Nollywood, Kannywood, Bollywood da ma Hollywood, tace kwanan nan zasu gana da masoyiyarta babbar jarumar Indiya wato Priyanka Chopra.

Za'a yi ganawa tsakanin Rahama Sadau da Priyanka Chopra ta Indiya
Za'a yi ganawa tsakanin Rahama Sadau da Priyanka Chopra ta Indiya

Rahma ta ce dama ita duk duniyar Indiya babu jarumar da tayi mata kamar Priyanka, domin ko tana yarinya ma Priyanka ake ce mata.

'Soyayya ta da wannan jaruma ne ma ya kaini ga shiga harkar fim din Hausa tun asali' inji Rahama.

KU KARANTA KUMA: Sheikh EL-Zakzaki ya sha kasa yau a kotu

An dai taba korar jaruma Rahma daga Indostiri kan rungumar wani yaro kirista a wakarsu, duk da cewa mazan fim suna abin da ya fi haka amma ba'ayi musu korar kare ba.

Rahama ta tabbatar cewa, ma'aikatanta da na jaruma Priyanka suna ganawa kan batun harkar fim, ta kuma saki sakon da jarumar tayi mata tun a baya, inda tace dama su kan gaisa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel