Ambaliyar ruwan sama ya lalata dukiyoyi a jihar Gombe
- Ambaliyar ruwan sama ya halaka gidaje da dukiyoyi da dama a jihar Gombe
- Ya kuma rusa gadar tafiya Biu daga Gombe
- A ranar Laraba ne aka sha ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar
Ambaliyar ruwan sama ya halaka gidaje da dukiyoyi da dama a jihar Gombe sannan kuma ya rufta gadar tafiya Biu daga jihar ta Gombe.
Ruwan sama ya fara zuba kamar dab akin kwarya a safiyar ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, sannan kuma an shafe saóí da dama ana zuba ruwan wanda hakan ya yi sanadiyar da ruwan ya shiga unguwanni takwas sannan kuma ya halaka dukiyoyi da gonakin alúmma.
Shugaban hukumar kula da ayyukan bada agajin gaggawa wato SEMA, Malam Mohammed Garba ya bayyana cewa ruwan saman ya haifar da cunkoso ga ababen hawa inda motoci ke tafiya a sahu daya sakamakon ruftawar gadar.
KU KARANTA KUMA: Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun
Malam Garba ya kara da cewa ba’a rasa rai a ambaliyar ba amma wani wanda ke zaune a unguwar Lili dake kusa da gadar ya bayyana tsintar gawar wani yaro dan almajiri mai shekaru 16 a karkashin gada.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng