Magani a gonar yaro: Anfanin goruba 5 a jikin dan adam
Bishiyar Goruba dai ta shahara a bakin mutane musamman ma yara inda a kasashe da dama na Afrika suke shan ta.
A kasar Hausa ma dai ana anfanin da dukkan abin da ya jibanci bishiyar ta goruba kama daga ganyen ta zuwa ya'yanta har ma da itccen nata.
Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin anfanin da gorubar takeyi a jikin dan adam:
1. Bincike ya nuna shan garin gorubar a cikin ruwan zafi na maganin cutar Asma.
2. Haka ma cin gorubar yakan hana cutuka irin na ciwon zuciya.
3. Shakar hayakin goruba da aka kona yana maganin ciwon hawan jini kamar yadda wasu suke fada.
4. Haka ma ance tana maganin cutar nan da ta addabi mutane ta basir.
5. Ance goruba tana hana dan adam kamuwa da cutar kansa.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng