Ciniki yayi kyau: Arsenal ta sayi ɗan wasan gaba daya ci ƙwallaye 113 a wasanni 183

Ciniki yayi kyau: Arsenal ta sayi ɗan wasan gaba daya ci ƙwallaye 113 a wasanni 183

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da kammala cinikin sabon dan wasan gaba na kasar Faransa Alexandre Lacazette daga kungiyar Lyon akan kudi pan miliyan 52.

Ana sa ran Lacazette mai shekaru 26 zai dinga amsan albashin pan 150,000 a kowane sati. Don haka Legit.ng ta kawo muku muhimman ababen lura game da wannan dan wasa.

KU KARANTA: Sheriff ya zargi tsofaffin ministocin gwamnatin PDP da satar kuɗin Al’umma

1- Yan uwansa yan kwallo ne

Duk dayake mahaifin Alez ba dan kwallo bane, amma yayansa da yaron kanin mahaifinsa dukkaninsu yan kwallo ne.

Ciniki yayi kyau: Arsenal ta sayi ɗan wasan gaba daya ci ƙwallaye 113 a wasanni 183
Lacazette

2- Ya san zare

A yanzu haka Lacazette na daya daga cikin zakakuran yan wasan gaba a nahiyar Turai, inda yazura kwallaye 113 cikin wasanni 183.

3- Bai buga wasanni dayawa ma Kungiyar Faransa wasa ba

Sai dai duk da iya cin kwallayensa, wasanni 11 kacal ya buga ma kungiyar kasar Faransa shekaru 4, daga 2013 zuwa 2017, inda ya zura kwallo daya kacal.

4- Dan wasan gaba mafi kwazo a tarihin kasar Faransa

Duk da cewa Lacazette bai tabuka komai a kungiyar kasar Faransa ba, amma tarihi ya nuna baya da Jean-Pierre Papin, shine dan wasa na biyu daya zura kwallaye 28 a shekara daya.

Ciniki yayi kyau: Arsenal ta sayi ɗan wasan gaba daya ci ƙwallaye 113 a wasanni 183
Lacazette

5- Zakaran gasar yan kasa da shekaru 19 na Duniya

Lacazette ne ya zura kwallon data baiwa kasar Faransa nasarar doke kasar Sifaniya a gasar yan kasa da shekaru 19 na nahiyar Turai.

6- Dan gatan Kocawa

An tabbatar da cewa Lacazette dan wasa ne bai bin umarnin kocawansa, hakan ne ya sanya shi zaman dan gata a wajen masu horar da yan kwallo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Daga masu karatu:

Asali: Legit.ng

Online view pixel