Obasanjo: Ban yi nadaman ritaya jami’an sojoji 'yan siyasa a shekarar 1999 ba – Inji Obasanjo
- Obasanjo ya ce bai yi nadama a kan ritayan da yayi ma wasu jami’an sojojin Najeriya
- Tsohon shugaban ya ce yayi wannan ne domin ya kare dimokuradiyya a kasar
- Obasanjo ya bayyana cewa yin haka zai taimaka wajen hana Najeriya daga wani yakin basasa
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ba shida wani uzuri ga ritayan wasu jami'an sojojin Najeriya wandanda suka sunduma a harakar siyasar kasar a shekarar 1999.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Obasanjo ya bayyana cewa, ya yanke wannan shawarar ne domin ya kare jaririyar dimokuradiyya a kasar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga watan Yuli a lokacin gabatar da wani littafi mai suna: "The First Regular Combatant: Birgediya Zakari Maimalari, OFR" a Abuja. Llittafin da Haruna Yahaya ya rubuta.

KU KARANTA: Obasanjo tare da wasu gwamnoni sunyi ta’aziyya ga Ganduje kan mutuwar Danmasanin Kano
Obasanjo ya kara da cewa yiwa jami'an sojan masu alaka da ‘yan siyasa ritaya zai taimaka wajen hana Najeriya daga wani yakin basasa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng