Dakarun Soji sun hallaka sojojin haya na Boko Haram a ƙauyen Gulumba (HOTUNA)

Dakarun Soji sun hallaka sojojin haya na Boko Haram a ƙauyen Gulumba (HOTUNA)

- Sojoji sun yi dauki ba dadi da Sojojin haya na Boko Haram

- An kashe yan Boko Haram da dama, an kashe Soja daya

Dakarun Sojin Najeriya sun samu nasarar karkashe wasu mayakan kungiyar Boko Haram da aka yiyo sojan hayansu daga makwabtan kasashe yayin wata arangama da suka yi a kauyen Gulumba.

Kaakakin rundunar Sojan kasa, Birgediya SK Usman ne ya bayyana haka inda yace suna tunanin Sojojin hayan sun fito ne daga tsagin Boko Haram dake karkashin jagorancin Mamman Nur.

KU KARANTA: Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 150 tare da asarar gidaje 1,233 a jihar Kros Ribas

SK Usman yace Sojojin Najeriya sun hallaka gaba daya mayakan na Boko Haram tare da kwato makamai masu dimbin yawa da suka hada da AK 47 guda 2, alburusai, bamabamai guda 2 da wayar hannu.

Dakarun Soji sun hallaka sojojin haya na Boko Haram a ƙauyen Gulumba (HOTUNA)
Makamansu

Haka zalika, Legit.ng ta ruwaito SK Usman yana fadin Sojojin Bataliya ta 3 dake Logomanu karamar hukumar Dikwa sun hallaka yan Boko Haram guda 3 tare da kwato makaman AK-47 guda 3, sai dai Soja daya ya rasu yayin karan battan.

Ga sauran hotunan:

Dakarun Soji sun hallaka sojojin haya na Boko Haram a ƙauyen Gulumba (HOTUNA)
Sojan haya na Boko Haram

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata kasa zata koma idan ka bar Najeriya?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng