Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA

Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA

- Hukumar NDLEA ta koka kan karuwar mashayan kwaya a tsakanin yan mata

- Hukumar tace ba wai yan mata kada bane, har da matan aure

Ana yawan samun karuwar shan kwayoyi a tsakanin yan mata da matan aure a jihar Borno, inji hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA.

Sai dai hukumar NDLEA ta danganta yawaitan shan kwayoyi da matsalar tsaro ta Boko Haram data addabi jihar shekara da shekaru, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

Shugaban NDLEA reshen jihar Borno, Joseph Iweajunwa yace yawancin matan aure da yan mata na shan Tramadol da Kodin ne domin samun karfi a jiki, sa’annan ya koka kan yadda ake samun mutuwa sakamakon shaye shayen.

Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA
Ýan mata da matan Aure

Shugaban yace daga watan Janairu zuwa Yuni an kama masu fataucin miyagun kwayoyi su 248, inda aka kama tabar wiwi mai nauyin kilo 336 da sauran kayan maye kamar su Tramadol, Diazepam, Exol, kodin da Rophynol.

Daga karshe, Shugaban NDLEA yace lallai sai gwamnati ta dage wajen antaya ma hukumar kudade domin yaki da miyagun kwayoyi tare da kira ga dukkan al’umma da a hada karfi da karfe wajen yakar wannan mummunan hali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani minista ya kamata Buhari ya sallama?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng