Yan matan Chibok: Buratai ya fadi dalilin da yasa akayi musanyan mutane da yan Boko Haram

Yan matan Chibok: Buratai ya fadi dalilin da yasa akayi musanyan mutane da yan Boko Haram

-Matakin yin musanya yazo ne daga gwamnatin tarayya ba daga soji ba – inji Buratai

-Gwamnatin tarayya tayi musanya da yan Boko Haram ne domin ceton yan matan Chibok

-Munci gallaba akan yan Boko Haram domin yanzu basu iya kai hari a wasu garuruwa illa Borno da Yobe kawai

Shugaban hafsin soji, Laftanat Janar Tukur Buratai yace anyi musanyan da mayakan Boko Haram ne domin a karbo kashi na biyu daga cikin yan mata guda 82 da aka kame a makarantar su a chibok, yace wannan musanya da akayi mataki ne wanda gwamnatin tarayya ta dauka ba soji ba.

Ya fadi hakan ne a wani shirin BBC mai suna Hard Talk a ranar Talata, shugaban hafsin sojin yace gwamnatin tarayya a lokacin ta gamsu cewa musanyan mayakan da yan matan shine abin da yafi dacewa.

Yan matan Chibok: Buratai ya fadi dalilin da yasa akayi musanyan mutane da yan Boko Haram
Yan matan Chibok: Buratai ya fadi dalilin da yasa akayi musanyan mutane da yan Boko Haram

Kamar yadda Buratai ya bayyana, “Ni dai ina ganin munyi aikin mu domin ceton yan matan Chibok din.

“Musanyan mayakan Boko Haram da yan matan Chibok mataki ne da gwamnatin tarayya da dauka ba sojin Najeriya ba. Shine matakin da gwamnatin ta ga yafi dacewa a wannan lokacin.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya tasanma ceton Dino Melaye daga kiranye na al'ummarsa

A yadda na dubi al’amarin, yana da fa’idoji; abin da ake nema shine a ceton yan matan.

“Bana tsamanin akwai wanda yace an kauda Boko Haram baki daya, domin ta’adanci abu ne mai matukar wuyan magancewa.

Buratai yayi nuni da cewa gazawar Boko Haram na kai hare-hare a babban birnin tarayya, Abuja, da wasu jihohin arewacin Najeriya kamar yadda suke yi kafin Mayun shekaran 2015, ya nuna cewa an ci galabar akan su sosai.

Kafin Mayun shekaran 2015, mayakan Boko Haram din suna kai hari a Abuja, kaduna da Kano. Har ma suna kokarin tsallakawa kudu. Ya zama dole mu dakattar da su.

Kusan shekara daya da rabi da ya wuce, basu kai hari a jihar Kano, Jos, Abuja da wasu jihohin ba, har ma jihar Gombe yanzu basu kai hari.

“Suna kai hari ne kawai a wasu bangarorin jihar Borno da Yobe.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel