Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar

Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar

- 'Yan ta'addan boko haram sun sake kai hari a wani kauye a Garin Diffa dake Jamhuriyar Nijar.

- Sun kashe mutane 9 sannan sun yi garkuwa da wasu mata da dama

- Duk da matakan tsaron da ake gudanarwa, Boko Haram sun cigaba da kai hare-hare a Kauyuka.

'Yan Boko haram sun sake kai hari a ranar lahadin da ta gabata a wani kauye a garin diffa take kudu maso gabashin yamma a jahar nijar.

Sun kasha akalla mutane 9, sun yi garkuwa da murtane kimanin 37 wanda ya hada da mata da yara. Duk da rundunar sojoji da matakan tsaron da ake gudanarwa, sun cigaba da kai hare-hare a garuruwa.

Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar
Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar

Gwamnan Diffa Dan Dano ya bayyana afkuwar hakan ne, kuma yace za a kokarta aga an kwato matan da suka yi garkuwa da su, don a yanzu haka rundunar soji sun kai tsaro kauyen.

KU KARANTA KUMA: Annobar shaye shayen kwaya a Najeriya

A shekarun baya da suka gabata, wasu 'yan ta'addacin Boko Haram sun taba kai hari a garin Diffa na Jahar Nijar. Mutane da yawa sun rasa muhallin su wanda yaja suka bar gidajensu don neman tudun tsira.

A sanadiyyar hare-haren da Boko Haram suke kai wa, mutane da dama sun rasa rayukan su, wasu kuma sun rasa muhallin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel