Maganganu 10 masu ɗauke da darussa daga bakin sarkin Magana, Maitama Sule

Maganganu 10 masu ɗauke da darussa daga bakin sarkin Magana, Maitama Sule

Tun bayan rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Dan Masanin Kano a ranar Litinin 3 ga watan Yuli, ta’aziyyar nata kwararowa daga bakunan al’ummar kasar nan, inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa.

Maganganu 10 masu ɗauke da darussa daga bakin sarkin Magana, Maitama Sule
Maitama Sule

Wata halayya ta Maitama itace iya magana da azanci, wanda hakan ya sanya Legit.ng kawo muku wasu daga cikin wasu maganganu masu cike da hikima da yayi a rayuwarsa. Asha karatu lafiya.

Ra’ayinsa dangane da Legas:

“Legas gida ne a waje na, na kasance ina zama a Legas fiye da Kano, ina son Legas saboda mutanen Legas na kauna ta, har sarauta aka yi min ta Onikoyi na garin Ikoyi, da kuma Bada na Legas, bugu da kari nine Ada Ida Akei Igburutu na Calabar."

KU KARANTA: Abubuwan tarihi 11 dangane da marigayi Dan Masanin Kano-KARANTA

Ra’ayinsa game da Kankan da kai:

“A rayuwa, idan kana da Kankan da kai, idan kana da saukin kai, idan kai mai raha ne, idan kana girmama mutane, idan kana kaunar jama’a, suma zasu kaunace ka, su girmama ka, kuma su so ka.

Game da bambamce bambamce:

“Gaba daya yan Najeriya na kaunata, kuma bani da dalilin kin su, dole ne in kaunace su, ni fa ba dan Kano bane kadai, ni bayarabe ne, ni dan kabilar Ibo ne, ni Ijaw ne, ni Kanuri ne, ni Fulani ne, ni Ibibio ne, ni Tiv ne, kai ni dafa duka ne. ina girmama kowa.”

Sha’awarsa ga siyasa:

“Sardauna ya taba kira nay a bukace ni in zama sakatarensa, na ki, yace sun zabe ni in tafi Landan don yin karatun shari’a, nace masa bana so. Sai ya tambaye ni “Wai kai me kake so?” nace masa “Abinda kake yi”

Alakarsa da Awolowo:

“Awolowo mutum ne mai alfahari, ya kan yi duk abinda yake so ba tare da karbar shawarata ba, ya taba yin korafi wai Arewa basa kaunarsa, kuma na bashi shawarar ya daina yin wasu abubuwa, amma yaki ji. Amma fa akwai akida, baya karya.”

Game da Arziki na Haram:

“Shuwagabannin mu a yau kudi suke nema a mulki, babu yadda za’ayi ka samu dukiya kuma kayi mutunci a lokaci guda. Shuwagabanninmu na da na son mulki ne don su bauta ma jama’a.”

Game da babbar bukatar Najeriya:

“Na sha fada, ina nanatawa, abinda muke bukata a Najeriya shine shugabanci, ba mulkin mallaka ba.”

Ra’ayinsa game da Matasan Najeriya:

“Ana bukatar kwarewar dattawa, saboda hadakar matasa da dattawa itace tushen cin nasara.”

Dangane da Rayuwa:

“Mu din dai, mune abin tambaya game da rayuwarmu, don haka mu zamu tafiyar da son ran mu.”

Halin da kasa ke ciki:

“Ba’a karrama masu gaskiya a al’ummarmu, mutane da dama sun son ballewa, babu amfanin falsafa a Najeriya, tsoro ya mamaye kasa, rikicin siyasan shi muke gani a kullum, tabarbarewar tarbiyya ya zama ruwan dare a al’umma, rashawa ta dukar da tattalin arzikin mu, bama iya sarrafa al’ada kanta.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin zaka taimaka ma Buhari ya samu waraka daga cutar dake damunsa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel