Tuni Najeriya ta fara amfani da sabuwar maganin kwaya cutar HIV – Inji gwamnatin tarayya
- Gwamnatin tarayya ta ce an fara amfani da sabon maganin kwaya cutar HIV a Najeriya kafin a kaddamar a yankin Afrika
- Unitaid ta kaddamar da sabon samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika
- Fiye da mutane miliyan 3 ke fama da kwaya cutar HIV a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce tuni ‘yan Najeriya sun fara amfani da sabon samfurin maganin kwaya cutar HIV da aka kaddamar a yankin Afrika mai suna Dolutegravir (DTG), amma ko da yake masu karfin arziki kawai suka iya saya saboda tsadarta.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, maganin DTG zai iya inganta da kuma tsawanta rayukan mutanen da suke fama da juriya daga wasu jiyya da kuma masu kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.
A wata rahoto a makon da ta gabata, ta bayyana cewa, wani kungiyar kiwon lafiya ta duniya,Unitaid ta kaddamar da sabon samfurin maganin kwaya cutar HIV a yankin Afrika wanda ake san ran za a sayar akan farashi mai rahusa ga mabukata.
A cewar rahoton, DTG da farko dai an amince da ita ne a Amurka a shekara 2013, yanzu haka marasa lafiyar 20,000 aka bai wa maganin a Kenya.
KU KARANTA: Matasa sun ba shugaba Buhari wa’adin makonni 8 ya yi murabus
Unitaid ta ce ana tsamani a wannan shekara ta 2017 maganin zai isa kasashen Najeriya da Uganda. Amma gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tuni ‘yan Najeriya sun fara amfani da sabon maganin a kasar tun kungiyar bata kaddamar da nata samfurin maganin ba.
Fiye da mutane miliyan 3 ke fama da wannan kwaya cutar HIV a Najeriya kuma kasa na biyu na mafi yawan masu rayuwa tare da HIV / AIDS a duniya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Har kana gani wadannan alamomin, toh, anzarta ka je ka yi gwajin HIV / AIDS
Asali: Legit.ng