Hukumar kiyaye hadura ta tura masu aikata laifuka kan titi 80 zuwa asibitin mahaukata
- Hukumar kiyaye hadura ta tura mutane 80 zuwa asibitin mahaukata
- Wadanda aka tura dai an same su ne da laifin karya dokar titi
- Hukumar ta kiyaye hadura ta tura su ne domin a duba kwakwalwar su
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa watau Federal Road Safety Corps (FRSC) a turance ta ce ta tura mutane 80 zuwa aibitin mahaukata domin duba lafiyar kwakwalwarsu.
Hukumar ta ce mutanen da suka maka asibitin an same su ne da karya dokokin titi daban-daban cikin wanaki biyu kacal.
Mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem shine ya bayyana wa manema labarai hakan.
Legit.ng ta samu labarin cewa Hukumar ta ce wannan tsari zai taimaka wajen rage aikata laifuffukan kan hanya, ya kuma dawo da lafiya ga titinan Nijeriya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng