An zo garin mu an ci mu da yaƙi: Ɗan Chanis ya gurgunta dan Najeriya da duka a jihar Ogun
- Wani dan Najeriya William Ekanem ya gamu da fushin dan China a Ogun
- Dan Chinan ya karyasa, sa'annan ya biya diyyar naira miliyan 3
Wani dan Najeriya William Ekanem ma’aikacin kamfanin kafinta na Bedmate Furniture Company dake Magboro jihar Ogun ya samu nakasa bayan da wani shugaban Kamfanin dan kasar Sin yayi masa duka ta hanyar fadar Kung Fu!
Hakan kuwa ya biyo bayan wata takaddama ne data faru tsakanin Ekanem da maigidansa Master Wan, a watan Afrilu, yayin da Ekanem ya siyo ya siya kayan abinci, kuma ya shigo dasu kamfanin, amma sai Master Wan ya bukaci ya san ko menene a cikin jakan.
KU KARANTA: Minista Audu Ogbeh ya cika alƙawari: Najeriya ta fitar da doya cikin sunduƙai zuwa ƙasarAmurka (HOTUNA)
Shi kuma Ekanem yaki ya, amma Wan ya matsa lallai sai yaga abin dake ciki, inda yayi amfani da karfin tuwa ya bude jakar, sa’annan ya wawwatsa masa kafafuwa a kirji da gadon bayansa kamar yadda ake yi a fadar Kungfu.
Jaridar Punch ta ruwaito nan take Ekanem ya baje sumamme, inda aka garzaya da shi Asibiti, daga bisani kuma aka sallame shi amma babu wanda ya biya kudin jinyarsa.
Sakamakon faruwar wanna lamari ya sanya ma’aikatar kwadago shiga cikin maganar, inda bayan anyi zaman farko tsakanin dukkanin wadanda abin ya shafa, sai kamfanin ta dauki nauyin biyan Ekanem naira miliyan 3.
Amma majiyar Legit.ng ta ruwaito kamfanin ta bakin lauyanta Ayo Durojaiye tana fadin dama can Ekanem ya saba yi musu sata, sa’annan kuma shi da kansa ya ji ma kansa ciwo, babu wanda ya buge shi.
Lauyan Ekanem, Emeruwa ya shaida cewar “An baiwa Ekanem takardar izinin amsar kudi na bankin Zenith, za’a cake masa kudadensa nan bada dadewa ba.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli dakin da Ojukwu ya boye yayin yakin basasa
Asali: Legit.ng