Hotuna: Gwamna Tambuwal ya ziyarci Shagari da tsofafin gwamnonin jihar sokoto
-Gwamna Aminu Tambuwal ya kai ziyaran taya murnar sallah karama
-Gwamna Aminu Tambuwal ya ziyarci tsohon shugaban kasan Najeriya Alh. Shehu Shagari
-Gwamna Aminu Tambuwal ya ziyarci tsofafin gwamnonin jihar sokoto
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci tsohon shugaban kasan Najeriya Alh. Shehu Shagari da kuma sauran tsofafin gwamnonin jihar Sokoton domin taya su murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya da kuma taya su farin cikin shagulgulan Sallah karama.

Sauran wadanda gwamnan ya ziyarta sun hada da Alhaji Garba Nadama, Malam Yahaya Abdulkarim, Dr. Attahiru Dalhatu Bafarawa da kuma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.






Allah ya maimaita mana. Ameen.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng