Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan sake fasalin tsarin Najeriya

Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan sake fasalin tsarin Najeriya

- Karuwar masu neman a raba kasar Najeriya ya sa an soma kiran a sake fasalin tsarin mulkin kasar

- Dakta Abubakar Umar ya ce ma'anar sake fasalin tsarin mulki nufin duk wani arziki dake wani yankin kasar bai kamata ya zama na gwamnatin tarayya gaba daya ba

- Alhaji Aliyu Sale Bagare ya ce Allah ne kadai ya san dalilin da yasa ya dunkule kasar Najeriya ta zama kasa daya

Kamar yadda kiraye kiraye kan a sake fasalin tsarin mulkin Najeriya domin a samu zaman lafiya ke karuwa a kasar.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Dakta Abubakar Umar masanin kimiyar siyasa na Jami'ar Abuja a cikin hirarsa da Muryar Amurka ya bayyana asalin ma'anar sake fasalin tsarin mulkin kasar.

A cewar Kari yayin da yake fasara sake fasalin mulkin kasa, ya ce wannan na nufin duk wani arziki dake wani yankin kasar bai kamata ya zama na gwamnatin tarayya gaba daya ba kamar yanda take yanzu, a nan arzikin dake yankin malakar na wannan yankin ne.

Ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya kan sake fasalin tsarin Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo

Dakta Kari ya ci gaba da cewa: "Abun da yankin ko lardin zai yi shi ne ya dinga biyan gwamnatin tarayya wani kaso na haraji da duk abun da ya samu lokaci zuwa lokaci. Hakan nan zai sa kowa ya ci gashin kansa."

Wasu 'yan siyasa a Najeriya kuma ba su amince da wannan tsari ba kamar irinsu Alhaji Aliyu Sale Bagare tsohon mataimakin gwamnan jihar Yobe suna da ra'ayi daban, ya ce tsarin da Najeriya ke kai yanzu haka baya bukatar wani garambawul, tsarin ta dace da ita.

KU KARANTA: 2019: Kwankwasawan jihar Katsina sun yi kira da babban murya ga Sanata Kwankwaso

Tsohon mataimakin gwamnan ya ce: “ duk wanda yake son a sake tsarin mulkin Najeriya, toh za a iya kiran mai shi "babban maci amanar kasa" domin ire irensu basu san gwagwarmayar da shugabannin mu na farko suka yi kafin kasar ta samu 'yanci daga turawan mulkin mallaka”.

Bagare ya ci gaba da cewa Allah ne kadai ya san dalilin da yasa ya dunkule kasar Najeriya ta zama kasa daya, kuma ka a nema a wargaje ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng