Kalli hirar da aka yi da Abba kyari, ɗansandan daya kama Evans da hannunsa (Hotuna/bidiyo)

Kalli hirar da aka yi da Abba kyari, ɗansandan daya kama Evans da hannunsa (Hotuna/bidiyo)

Jarumin jami’in dansandan daya jagoranci farautan fitaccen mai garkuwa da mutan Evans, Mataimakin kwamishina Abba Kyari ya bayyana cewa ba karamin aiki suka yi ba kafin su samu nasarar cafke sa.

Abba Kyari ya bayyana haka ne ga BBC Hausa, inda yace “A baya Evans ya gagari dukkanin jami’an tsaron Najeriya har na tsawon shekaru bakwai.”

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta tattara ma gwamnati naira biliyan 239 a watanni 4

A watan Yunin da muke ciki ne dai Evans ya fada tarkon Yansanda bayan kwashe kimanin shekaru bakwai zakara na bashi sa’a.

Kalli hirar da aka yi da Abba kyari, ɗansandan daya kama Evans da hannunsa (Hotuna/bidiyo)
Abba kyari

Kyari yace duk da irin bincike da hukumar Yansanda tayi akan Evans, basu samu nasarar kama koda abokansa ba.

Saurari hirar da aka yi da shi a nan:

Kalli hirar da aka yi da Abba kyari, ɗansandan daya kama Evans da hannunsa (Hotuna/bidiyo)
Abba Kyari tare da Evans

Wani abin mamaki da Abba Kyari ya bayyana ma majiyar Legit.ng shine cewa “Evans ya kwashe sama da shekaru 20 yana aikata miyagun laifuka a kasar nan, kwararre ne, kuma yana da layukan waya da suka haura 100.”

Kalli hirar da aka yi da Abba kyari, ɗansandan daya kama Evans da hannunsa (Hotuna/bidiyo)
Yayin da aka yi ma Kyari karin girma

A yanzu dai hukumar Yansanda na gabatar da bincike kan Evans, inda daga bisani kuma zata gurfanar da shi gaban kuliyan manta sabo, wato Kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me ya dace ayi ma Evans?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng