Hanyoyin 6 da Buhari yayi wa ‘yan Najeriya fatar alheri a sakon karamar Sallah

Hanyoyin 6 da Buhari yayi wa ‘yan Najeriya fatar alheri a sakon karamar Sallah

- Abubuwan alheri 6 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rokawa ‘yan Najeriya

- Shugaba Buhari ya yi addu’a Allah ya ba kasar Najeriya zaman lafiya

- Buhar ya gode wa wadanda suka yi masa addu’a a cikin watan Ramadan

1. Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su nizanci yada labaran karya wanda zai iya haddasa hargitsi a cikin ƙasar.

2. Buhari yayi wa al’umman musulmai fatan alheri da kuma taya su murnar karamar Sallah. Shugaban ya kuma yi addu'a ga Allah mai girma da ya karbi ibadan da muka yi a cikin watan Ramadan gaba daya.

3. Shugaban ya yi addu'a da cewa Allah yaba kasar Najeriya zaman lafiya, kuma yasa a yi bikin a cikin lumana.

Hanyoyin 6 da Buhari yayi wa ‘yan Najeriya fatar alheri a sakon Sallar Idi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

4. Shugaban ya yi addu'a da cewa Allah ya ba gwamnatinsa karfin gwiwa a kan alkawuran da yayi wa al’umman kasar da kuma samar da mafita ga matsalolin da kasar ke cikin yanzu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aikawa 'yan Najeriya sakon barka da Sallah

5. Buhari ya yi addu’a da cewa Allah ya wadata kasar da abinci a tsawake.

6. Shugaban yace ya gode wa waɗanda suka tuna da shi a cikin addu’o’in su, kuma suka roka masa samun lafiya a cikin wata mai tsarki.

Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tuni ya aikawa musulmai da kiristocin Najeriya sakon gaisuwa a yayin bikin sallah daga Landan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng