Shin mutum nawa ne a Najeriya? Jaridar The Economist ta Turai tayi nazari

Shin mutum nawa ne a Najeriya? Jaridar The Economist ta Turai tayi nazari

- Shin nawa ne yawan mutanen Najeriya?!

- Dalilan da suka hana samun kidiya sahihiya

- Hukumar Kidiya ta 'kasa na bukatar biliyan 223 domin domin kidiya jama'a

Kasar Najeriya dai ta dade tana wa kanta Kirari da Taurariyar Afirka. A bisa kididiga na shekarar 2015, an 'kiyasta yawan mutanen Najeriya a kalla Million 182. Wannan kididigan yasa ana hasashen cewa Najeriya zata zama kasa na uku a duniya wajen yawan al'umma bayan kasar China da India.

Toh amma wannan hasashe anyi shi bisa ga alkalluma da aka samu biyan kidaya na shekara 2003 wanda ake zargin an ruruta yawan jama'an. Dalilin yin wannan kari kuwa shine yan siyasa sun san cewa ana amfani da yawan jama'ar da ke garuruwansu ne domin wajen rabon madafan mulki da samun kudin kashewa daga gwanatin tarayya.

Shin mutum nawa ne a Najeriya? Jaridar The Economist ta Turai tayi nazari
Shin mutum nawa ne a Najeriya? Jaridar The Economist ta Turai tayi nazari

A shekara ta 2013, shugaban hukumar 'kidiya ta kasa(NPC) Mr Festus Odimegwu yace duk alkalluma na 'kidiya da akeyi a Najeriya basu bada sakomako sahihai, wannan maganar ce tayi sanidiyar marabus dinsa.

Kidiyan mutanen Najeriya dai tun bayan samu 'yancin kai abu ne mai sarkakiya. Dalili kuwa shine kasar dama tana rabe kashi biyu ne; Arewancin Najeriya wanda mafi rinjiye musulmi ne da kuma kudancin ta wanda yawancin mazauna can din mabiya addinin kirista ne. Kafin samun 'yancin kan Najeriya a shekara ta 1960, mutane sunyi ta zargin baturan Ingila da ruruta yawan mutanen arewa wanda suka fi nuna ma gata.

A shekara ta 1962, wasu alkalluma daga haramtaciyar 'kidaya da akayi a wasu jihohin kudancin Najeriya sun nuna cewa yawan mutanen kudun ya rubunya da har ta percent 200 a cikin shekaru goma. Ba'a samu cikaken bayanin 'kidayar ba amma shugabanin arewa sunyi watsi da wannan alkalluman sannan daga bisani suka sake yin wata 'Kidayar wanda ta sake nuna wa cewa dai arewa tana nan kan gaba wajen yawan al'umma.

Wannan hatsaniyar ne ta jawo yin juyin mulkin da sojoji sukayi ta yi da kuma yunkurin balle wa daga Najeriya da mutanen kudancin Najeriya sukayi da ya haifar da yakin basasa a kasar.

Tun daga wannan lokaci arewaci da kudancin Najeriya dai sun cigaba da yin kama-kama wajen mulkar kasar ko dayake babu wata doka a rubuce da ce dole hakan za'ayi.

Kidayar kasa da akayi na shekarar 1973 da 1991 duk anyi watsi dasu. A shekara ta 2006 anyi da kumfar baki bayan kidiyar da akayi ta nuna yawan mutanen da ke Jihar Kano sun kai miliyan 9.4 wanda ya 'dara takwarar ta yamma wato Jihar Legas da aka samu mutane miliyan 9 kawai. Jihar Legas din ta sake maimaita wani 'kidiyar ba tare da izinin Hukumar 'kidiya ta kasa ba inda ta fitar da alkalluma da ke nuna mutanen da ke Jihar Legas sun kai miliyan 19.

Anyi kokarin sake wata kidiyar amma abin yaci turra sai dai yanzu hukumar kidiyar ta kasa wato (NPC) tace za'a gudanar da wani kidiyar a shekara ta 2018 amma anyi kiyasin cewa zai hadiye kudin har naira biliyan 223 wanda a halin yanzu babu tabbas din samun irin wannan kudin.

A shekara ta 2006, wata kungiya mai suna Afrocapolis wanda mallakar Faransa ne tayi yunkurin yin kidayan ta hanyar amfani da tauraron dan adam (satelite) amma sai sakamakon ta suka fara samu yazo da tangarda domin ya saba ma duk wani kidiya da akayi daga baya. Daga baya masu binciken sun lura cewa basu yi la'akari da yadda wasu garuruwan suka kara zama birane bane.

Idan dai har ba'a samu sahihiyan hanya da za'abi wajen kididigan jama'ar Najeriya ba tare da nuna fifiko ko kyama ga wani bangare ba, toh gwamnati ba zata iya aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen da zai amfana jama'a ba bisa ga bukatun ko wana bangare

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng