Cakwakiya: Tsoho mai shekaru 80 ya memi auren ‘yarshi (Karanta)

Cakwakiya: Tsoho mai shekaru 80 ya memi auren ‘yarshi (Karanta)

- An bayyana yadda wani tsoho mai shekaru 80 a kudancin Ghana ya nemi auren ‘yar shi bisa kuskure saboda bai iya gane ta ba.

- Togbui Asilenu dai ya na da mata 12 da ‘ya’ya da suka haura 100, amma ya ce wannan ba zai hana shi idan ya ga wata matar da yake so ya kara aure ba.

A wata hira da wakiliyar gidan talabijin din TV3’s, Potia Gabor ta yi da mutumin da iyalinsa a ranar ubanni ta duniya, ya bayyana cewa duk da ya tsufa, wannan ba yana nufin ya daina haihuwa ba kenan.

Legit.ng ta samu labarin cewa da aka bukaci ya jero sunayen ‘ya’yan na shi, Asilenu dai kasawa ya yi, anan ne daya daga cikin ‘yayan sa maza ya bayarda labarin yadda baban na shi ya nemi auren yar uwar shi a kwanakin baya.

Cakwakiya: Tsoho mai shekaru 80 ya memi auren ‘yarshi (Karanta)
Cakwakiya: Tsoho mai shekaru 80 ya memi auren ‘yarshi (Karanta)

Ya ce da ‘yar uwar ta shi ta fada wa baban cewa ita fa ‘ya shi ce, sai ya ce mata idonsa ne ya samu matsala shi ya sa ya kasa gane ta.

Banda rashin gane ‘yayan da Asilenu ke yi, haka zalika su ma ‘yayan ba su san adadin su ba, kuma ba su iya gane junan su gaba daya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng