Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya

Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya

Sarkin Saudi Arabia, Salman ya nada yaronsa Yarima Mohammed bn Salman a matsayin Yarima mai jiran gado bayan ya tumbuke yarima Mohammed bn Nayef.

Sarkin ya hada ma Yarima Mohammed Salman mukamin firaim minista da kuma minista tsaro, kuma tuni tsohon yarima mai jiran gado, Nayef yayi mubaya’a ga Yarima Mohammed bn Salman.

KU KARANTA: Kalli hotunan ziyarar da ýan Shi’a suka kai ma Shehi Dahiru Bauchi

Shi dai Yarima Mohammed Salman matashi ne mai shekaru 31 da haihuwa, kuma shine ya jagoranci yaki tsakanin Saudiya da kasar Yemen a lokacin dayake kula da ma’aikatar makamashin kasar Saudiya.

Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya
Sarkin Saudiyya Salman tare da yaronsa Mohammed

Legit.ng ta samo rahoton a ranar 31 ga watan Agusta na shekarar 1985 ne aka haifi Yarima Mohammed bn Salman, kuma shi ne babban dan matar Sarki Salman ta uku, Fahdah bint Falah bin Sultan.

Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya
Sabon Yarima mai jiran gado, tare da tsohon Yarima mai jiran gado

Har ila yau, Mohammed bn Salman ya karanci Ilimin shari'a a jami'ar Sarki Saud dake Saudiya kafin ya soma aiki da wasu ma'aikatun gwamnati, kuma yana da mata daya da 'ya'ya hudu, biyu mata biyu maza.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene matsayin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng