'Yan kungiyar asiri sun addabi jihar Kross Ribas
- Mazauna birnin Kalaba da sauran wasu manyan garuruwan jihar Kuros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya sun koka kan yadda 'yan kungiyoyin asiri ke addabar jihar.
- Wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC cewa rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin irin su Vikins da Mafiyas da KKK yana shafar harkokin yau da kullum, wani lokaci ma har ya kai ga asarar rayuka.
Wani mazaunin birnin ya gaya wa BBC cewa "Idan suka fama rikici komai tsayawa yake yi domin kuwa suna yin amfani da bindigogi. Shekaraniya sun far ma mutane rike da bindigogi; kowa hankalinsa a tashe yake".
Legit.ng ta samu labarin cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar Hafiz Muhammad Inuwa ya shaida wa BBC cewa rikici tsakanin kungiyoyin asiri a jihar ba sabon abu ba ne, yana mai cewa rundunarsa na daukar matakan kare lafiyar jama'a.

A cewarsa, "gaskiya rikici tsakanin wadannan kungiya ba wai yana hauhawa ba ne; dama wani lokaci sukan samu fadace-fadacen cikin gida har a kan rasa rayukan mutum daya ko biyu. Amma muna farautarsu har sai mun ga bayansu".
Babban jami'in 'yan sandan na jihar Kuros Riba ya ce jami'ansa sun kama 'yan kungiyar asiri da dama kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya domin yanke musu hukunci.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng