Wani azzalumi ya bugawa yaro kusa a kai saboda ya saci N500
Legit.ng taci karo da wani labara mai ban takaici inda wani dan maraya na asibiti yana jinya yanzu sanadiyar kusa inci 3 da wani yayanshi ya buga masa akai saboda kawai ya saci N500.
Game da cewan rahotanno, yaron mai suna Friday Paul, wanda ke zaune da yayanci a gida mai lamba 6, Anjolarin Street, Odogunyan, Ikorodu, ya sha ukuba ne saboda yayi masa sata.
Yaron ya fara zama da yayan nasa ne bayan iyayensa sun rasu shekaru 2 da suka gabata. Yaron yayi dan hali inda yayan ya tuhumcesa da daukan masa N500, kawai sai ya azabtar da shi.
Yayan mai suna Paul ya kai yaron cikin daki ya buga masa kusa inci 3 kai.
D makwabta suka ji iwun yaro a cikin gida, sai sai shiga gidan suka fitar da yaron da wuri zuwa asibitin Ikorodu inda suka ki karbansu saboda rashin kudi. Daga baya aka kai sa asibitin The Saviour The Rock.
KU KARANTA: Matasan Arewa sun fitar da yan takaran 2019
Mr. Paul ya arce daga gidan amma makwabta suka damkesa kuma suka yi masa dukan har suka kusa kasha shi kafin yan sanda suka cece shi.
Ana bukatan N100,000 domin yi masa aikin tiyata duk da cewa an cire kusan daga kansa.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng