Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare
- An bude wani masallaci na wasu da suka kira kansu masu sassaukar ra’ayi a Kasar Jamus
- Maza da mata ke sallah a gwamutse, sannan matan basa sanya mayafi
- An gina masallacin ne a jikin coci
An bude wani masallaci na wasu da suka kira kansu masu sassaukar ra’ayi a Kasar Jamus inda mata da maza suke sallah a tare.
Masallacin da aka sakawa suna Ibn Rushd-Goethe yana gine ne jikin wani cocin Protestant da ke birnin Berlin. Wannan masallaci shi ne irinsa na farko a kasar ta Jamus.
KU KARANTA KUMA: An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue Suswam akan zargin almundahana
A wannan masallaci, ‘yan Sunni da ‘yan Shi’a na yin ibada a tare kuma an sahalewa mata da su shiga masallacin tare da aiwatar da duk nau’in ibadar da suka yi niyya ba tare da sanya hijabi, mayafi ko kallabi ba.
![Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt6cr0gnec1n1.jpeg?v=1)
Wata mai kare ‘yancin mata, Seyran Ates, ta bayyana cewa sun shafe shekaru kusan takwas suna fafuttukar nemawa musulmai irin wannan wajen bauta amma abin ya gaggara sai a wannan karon Seyran Ates.
Ta bayyana ce wa: “Rashin hadin kai a wuraren bauta ne ke haddasa yawaitar ta’addanci da munanan ayyuka a addinin musulunci wanda kamata ya yi a ce mu musulman zamani mu hada kan mu awuraren bautarmu."
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng