Manyan ‘yan wasa sun halarci jana’izar Cheick Tiote (Hotuna)

Manyan ‘yan wasa sun halarci jana’izar Cheick Tiote (Hotuna)

- An yi bikin karshe na jana’izar dan wasan kasar Kodebuwa Cheick Tiote

- ‘Yan wasan kungiyoyin daban-daban suka halarci jana’izar

- Tiote ya mutu yana da shekaru 30 da haihuwa

An yi jana’izar shahararren tsohon dan wasan kwallon kafa nan ta kungiyar Newcastle Cheick Tiote a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni.

Shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa tsofoffi da kuma na yanzu na kasar Kodebuwa cikin su har da Kolo Toure, Salomon Kalou, da kuma Wilfried Bony sun kasance tare da iyali da kuma abokai marigayi tsohon dan kungiyar Newcastle ta kasar Ingila Cheick Tiote a wurin bikin jana’izar.

Dan wasan nan na Manchester United, Eric Bailly da kuma wasu ‘yan wasan gasar firimiyar sun kasance daga masu yin makokin marigayin.

Manyan ‘yan wasa sun halarci jana’izar Cheick Tiote (Hotuna)
Marigayi tsohon dan wasan kwallon kafa ta kungiyar Newcastle Cheick Tiote

An yi bikin tunawa da dan wasan a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, a Beijing, don girmama wa tsohon dan kwallon kafan.

Manyan ‘yan wasa sun halarci jana’izar Cheick Tiote (Hotuna)
A lokacin da ake shigowa da gawar Tiote a wajen bikin jana'izar

KU KARANTA: Manyan Arewa ne suka biya matasan Arewa don suyi barazana – Babafemi Ojudu

A cewar Legit.ng, Tiote ya mutu yana da shekaru 30 bayan da ya auka a lokacin zaman horo a wani kungiyar kwallon kafada da aka sani da Beijing Enterprise.

Manyan ‘yan wasa sun halarci jana’izar Cheick Tiote (Hotuna)
Eric Bailly dan wasan Manchester United na daga cikin masu zaman makoki

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyalan sahararren dan wasan dambe nan Anthony Oluwafemi Joshua a cikin wannan bidiyo

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng