Kungiyar Izala reshen karamar hukumar Potiskum ta tallafawa marayu da gajiyayyu

Kungiyar Izala reshen karamar hukumar Potiskum ta tallafawa marayu da gajiyayyu

A safiyar jiya Lahadi ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’Ikamatis Sunnah reshen karamar hukumar Potiskum jihar Yobe, ta kaddamar da tallafin marayu da gajiyayyu a cibiyar kungiyar wato Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Islamic Centre dake Hayin Gada a kan titin Kano a garin Potiskum.

Sheikh Nuruddeen A. Tukur Numan shine shugaban komitin marayun,kuma shine malamin da Kungiyar (jibwis) Ta kasa baki daya ta turoshi garin Potiskum jihar yobe domin gabatar da Tafsirin Al’qur’ani Mai girma. Kuma shine wanda ya fara mika tallafin ga marayun.

Kungiyar Izala reshen karamar hukumar Potiskum ta tallafawa marayu da gajiyayyu
Kungiyar Izala reshen karamar hukumar Potiskum ta tallafawa marayu da gajiyayyu

Legit.ng ta samu labarin cewa bujimin malamin ya yi jawabi mai ratsa zuciya awajen mika tallafin, Inda ya nunawa mahalarta taron muhimmacin tallafawa marayu da gajiyayyu, Inda ya ambaci wannan rana a matsayin ranar murna tare da farin ciki ga dukkan marayun Potiskum baki daya.

Sheikh Nuruddeen A. Tukur Numan ya ce wannan shekarar ba a taba tallafawa marayu wadanda a dadinsu yakai mutum 330 ba tare da gajiyayyu 60.

Sakataren kwmitin marayu, Malam Usman Jaji, ya tabbatarwa wakilinmu cewa sun rabawa marayun, inda kowane daya daga cikinsu ya sami tallafin shadda yadi biyar ko turmin zani.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng