Dubi wani mahaukaci da yake tsintar pampers na yara, sai wannan ya faru bayan kwanaki 14 (Hotuna)

Dubi wani mahaukaci da yake tsintar pampers na yara, sai wannan ya faru bayan kwanaki 14 (Hotuna)

- An cafke wani mahaukaci mai kwasan pampers na yara domin ya sayar wa wasu boka

- Mahaukaci ya ce bayan kwanaki 14 da kwasan pampers din, yaran za su mutu

- An wallafa hotunan wannan mahaukacin ne da kalaman sa a shafin zumunta ta Facebook na al'umma mazaunin Anambra

Wannan mahaukaci ya ce yana tsintar da pampers na yara da aka gama amfani da su a bololi daban-daban. Ya ce babu shaka bayan kwanaki 14 yaran za su mutu. An wallafa hotunan mahaukacin ne da kalaman sa a shafin zumunta ta Facebook na al'umma mazaunin Anambra a Asaba.

KU KARANTA: An sake sace wani babba a gwamnati don neman fansa

A cewar Legit.ng, an samu mahaukacin ne tare da wata jakar cike da pampers na yara da aka gama amfani da su wanda ya tattara daga wasu bololi da sunan neman abinci. A lokacin da ake tambayarsa, sai ya yi furuci da cewa yana sayar da su ga wani abokin cinikinsa da ke Jihar Ogun.

Dubi wani mahaukaci da yake tsintar pampers na yara, sai wannan ya faru bayan kwanaki 14 (Hotuna)
Mahaukaci da yake tsintar pampers na yara

Dubi wani mahaukaci da yake tsintar pampers na yara, sai wannan ya faru bayan kwanaki 14 (Hotuna)
Mahaukacin da yake tsintar pampers na yara ya bayyana cewa akwai abokin cinikinsa da yake sayar wa a Jihar Ogun

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari wani tsohon sojan Biyafara a lokacin yakin basasa inda ya ce yana da shekaru 21 ya shiga sojan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng