Lafiya uwar jiki: Ababan sha 3 da ya kamata mai azumi ya kauracewa (Karanta)

Lafiya uwar jiki: Ababan sha 3 da ya kamata mai azumi ya kauracewa (Karanta)

- Kaso 60 zuwa 70 a cikin dari na jikin dan Adam ya kunshi ruwa ne. Wannan ya sa a duk lokacin da mutum ya rage adadin ruwan da yake sha, hakan ka iya taba yadda jikin sa ke aiki.

- A yayin da muke azumi, mu kan rasa ruwa a jikin mu, wannan ya sa ya na da matukar muhimmanci mu maida adadin ruwan a lokacin shan ruwa da Sahur.

Rashin yin hakan zai iya haifar da cushewar jiki, ciwon kai, jin gajiya, bushewar fata da dai sauran su.

Wani lokacin a maimakon mu maida ruwan jikin, sai mu bige da shan abubuwan da ka iya rage wanda muke da shi.

Legit.ng ta samu daga majiyar mu cewa irin wadannan ababan sha sun hada da:

1. Shayi ko Kofi (Coffee):

Yawan shan shayi ko kofi ga mai azumi zai iya haifar da mara ido a sakamakon sinadarin ‘Caffein’ din sa suka kunsa. Sinadarin Caffein dai an san shi da tsotse ruwan jiki da sanya kishi ruwa.

2. Ababan sha masu gas:

Lemunan sha kamar su Coca cola, fanta, Sprite, Lacasera da sauran su da suka kunshi gas su kan sanya mutum ya ji koshi sosai ko da bai ci abincin kirki ba, sannan su kan dakile narkewar abinci a ciki. Rashin narkewar abinci da wuri kuwa matsalolin da yake haifar wa ba sa kirguwa. Wannan ya sa yafi kyautuwa mai Azumi ya guje su.

Lafiya uwar jiki: Ababan sha 3 da ya kamata mai azumi ya kauracewa (Karanta)
Lafiya uwar jiki: Ababan sha 3 da ya kamata mai azumi ya kauracewa (Karanta)

3. Ababen Sha masu sikari da yawa:

Wasu ababan shan basu da gas amma kuma suna da sikari da ya wuce kima. Su ma wadannan za su iya haifar wa mai azumi matsala musamman idan aka sha su a lokacin sahur. Dalili kuwa shi ne, su kan sa mutum ya ji yunwa da wuri.

Menene mutum mai azumi to ya kamata ya sha?

Amsar ita cefarin ruwa, ruwan ma kuma ba wanda ya ke da sanyi matuka ba. Sannan idan za a sha ruwan, kar a sha da yawa sosai a lokaci daya.

Sai kumaruwa daga kayan itatuwakamar su kankana ko kwakwa

Sannan a guji cin abinci masu yaji ko gishiri da yawa a yayin sahur, saboda su na kara wa mutum kishi.

A sha ruwa lafiya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng