An fassara Bible cikin harshen Tera dake jihar Gombe

An fassara Bible cikin harshen Tera dake jihar Gombe

- Kabilar Tera da ke jihar Gombe sun fassara littafi mai tsarki wato Bible cikin harshen su

- Kakakin majaklisar wakilai Yakubu Dogara na daya daga manyan bakin da suka halarci bakin kaddamar da fassarar

- Aikin fassarar ya dauki tsawon shekaru 10 kafin a kammala ta

- Shugaban sarakunan gargajiya kiristoci a arewacin Najeriya yayi kira ga sauran kabilu suyi koyi da wannan

Kakakin majaklisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara yace wadanda suka saurari wa'azi cikin harshensu sun fi rikewa.

An yabawa kabilar Tera cikin jihar Gombe saboda dawainiyar da suka dauka na fassara linjila cikin harshensu.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, kakakin majalisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara ne yayi wannan yabon lokacinda aka yi bikin kaddamar da fassarar, tareda wasu litattafai da aka kaddamar domin karfafa amfani da harshen Tera.

An fassara Bible cikin harshen Tera dake jihar Gombe
An fassara littafi mai tsarki Bible cikin harshen Tera

Mista Dogara ya ce wadanda aka yiwa wa’azi cikin harshen da suka sani ko da aka haife su da shi sun fi rike abunda suka ji.

KU KARANTA: Ana shirin haramta amfani da Nikabi a wata kasa

K.K. Lubo, wanda ya jaogranci fassarar ya ce aikin ya dauke shu shekaru 10 suna yi.

Mai Tangalang, shugaban sarakunan gargajiya kiristoci a arewacin Najeriya ya yaba da aikin, wanda yayi kira ga sauran kabilu suyi koyi da shi domin habaka harsunan da idan ba haka aka yi ba, zasu bace baki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari tsohon direban Bishof David Abioye na Living Faith Church wanda ya karbi

musulunci bayan ficewa daga cocin

Asali: Legit.ng

Online view pixel