An kama masu safarar 'yan mata daga Afirka zuwa Saudiyya

An kama masu safarar 'yan mata daga Afirka zuwa Saudiyya

- Hukumomin shige da fice a kasar Ghana sun cafke wasu mutane hudu da ake zargi da safarar 'yan mata 44 a kan hanyarsu ta ficewa daga kasar domin zuwa Saudi Arabia.

- Ana kai 'yan matan ne kasar Saudiyya da wasu kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya domin yin ayyukan gida.

Kakakin hukumar shige da fice na kasar, Mista Michael Amakou Attah, ya ce an kama mutanen ne a bakin iyakar kasar da Togo tare da 'yan matan a wasu motoci biyu kirar bas, a karshen makon da ya gabata.

Ghana ta haramta jigilar 'yan matan ta filin jiragen samanta, saboda abin da hukumomi suka kira wulakanci da cin zarafin da ake yi wa 'yan matan a kasashen.

Biyu daga cikin mutanen 'yan Ghana ne, sauran biyun kuma 'yan Najeriya ne.

An kama masu safarar 'yan mata daga Afirka zuwa Saudiyya
An kama masu safarar 'yan mata daga Afirka zuwa Saudiyya

Mista Michael ya ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka dauki nauyin safarar 'yan matan.

Galibi dai 'yan matan na fuskantar barazana iri-iri, ciki har da fyade da kisa a hanyarsu da zuwa kasashen da za a kai su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng