Zuwan ɗan wasa Griezman Man U, ta leko ta koma

Zuwan ɗan wasa Griezman Man U, ta leko ta koma

- Griezmann ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar Atletico Madrid

- Griezman ya kara shekara daya a zaman nasa a kungiyar

Fitaccen dan wasan nan dan kungiyar Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da gudanar da sana’ar kwallon kafa a kungiyar Atletico Madrid ta hanyar rattafa hannu akan sabon kwantaragi.

Griezman ya kara shekara daya a zaman nasa a kungiyar, wanda hakan ya kawo karshen rade-radin da aka dinga yi na cewa dan kwallon mai shekara 26, zai koma Manchester United.

KU KARANTA: Sanatocin Amurka sun hana siyar ma Najeriya makaman yaki

Sai dai Legit.ng na ganin kara tsawaita zaman na Greizman baya rasa nasaba da kin soke hukuncin hana kungiyar Atletico Madrid siyan sabbin 'yan wasan kwallon kafa da Fifa tayi.

Zuwan ɗan wasa Griezman Man U, ta leko ta koma
Griezman

Cikin hukuncin da FIFA ta yanke, Atletico ba za ta siya wani sabon dan kwallo ba har zuwa watan Janairu.

Griezman ya zura kwallaye 26 a kakar wasa data kammala, inda Atletico ta kare a mataki na uku a kan teburin gasar cin kofin Laliga, biye da Basalona da Real Madrid.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rayuwa tayi muni a garin nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel