Lafiya uwar jiki : Amfanin yawan shan ruwa 9 ga jikin dan Adam
Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman amfanonin ruwa 6 ga ruhin dan Adam a koda yaushe.
Masu magana sukace ruwa baka da makiyi. Shi ruwa wani sinadari ne da Allah mai jinkai ya baiwa bayinsa cikin sauki kuma a yawaice.Amma da yawanmu bamu san dimbin amfaninshi ba face gusar da kishi da kuma ayyukan yau da kullum.
Ga amfanin ruwa ga jikinmu:
1. Rage kiba
Shi ruwa bai da mai, bai da siga, kana kuma bai da sinadarin kalori, saboda haka shan shi koda yaushe yakan taimaka wajen rage kibar jiki.
2. Lafiyar zuciya
Game masu ilimin lafiyar zuciya, ruwan kan rage iwuwan samun ciwon zuciya da 41 cikin 100
3. Karfin jiki
Ruwa kan taimaka wajen karfin jiki saboda rashin shan sa kan kashe jikin mutum, ya maishe shi a gajiye.

4. Warkar da ciwon kai
Hasali abinda ke kawo ciwon kai shine rashin shan isasshen ruwa
5. Kyawun fatar jiki
Ruwa kan sa fatar jikin mutum ta dinga kyau tana kyalli a koda yaushe
KU KARANTA: Kasar Saudiyya ta hana yan kasan Qatar aikin Umrah
6. Cutan daji
Ruwan kan rage yiwuwan kamuwa da cutan dajin mafitsara da kasha 50 ciki 100
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng