Limamin Harami, Sheikh Sudais ya ƙulla abota da wani yaro ɗan Afirka

Limamin Harami, Sheikh Sudais ya ƙulla abota da wani yaro ɗan Afirka

-Tsananin bajinta ta sa Limamin Harami sumbatar yaro dan Afirka

- Wannan yaro ya zamto zakaran gwajin dafi ne a gasar Al-Qur’ani

Limamin masallacin Harami Shaykh Abdulrahman Sudais ya sumbaci goshin yaron nan (Amer Falatah) ya kuma fada masa cewa insha Allah shine zai zama limamin Harami nan gaba.

Wannan yaro dan Albarka, Ameer Falatah ya zamto abin Alfahari ga mahaifansa da Musulinci, har ma ga Musulmin duniya, Yaron ya taka rawar gani ne a musabakar Alqur'ani data gudana a tsakanin gagga gaggan hafizan Duniya gaba daya.

KU KARANTA: Jana’izar dan kwallo Tiote: Jama’a sun koka (Hotuna/bidiyo)

Ko a baya ma an samu wani gwanin hadda daga kasar Najeriya wanda ya lashe kambun gasar Al-Qur’ani, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Limamin Harami, Sheikh Sudais ya ƙulla abota da wani yaro ɗan Afirka
Sheikh Sudais tare da yaron

Yawanci hazikan gasar Al-Qur’ani suna samun kyautan kujerar Makkah ne kacal a Najeriya, amma Sheikh Sudais yayi ma Hafizi Ameer fatan ya zama limamin masallacin harami inshaa Allah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda yaron Fasto ya muslunta

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng