Tashin hankali yayinda gadar Jebba ya rushe
Abun tashin hankali ya afku a hanyar Jebba yayinda gadar dake kauyen Tatabu kilomita 15 daga hanyar Mokwa Jebba ya rushe sakamakon ruwa da akayi kamar da bakin kwarya.
Kalli hotunan gadar da ya rushe a kasa:
KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS ta damke masu garkuwa da mutanen da suka addabi jama’a
Rushewar gadar ya hana motoci tafiya daga bangarorin guda biyu na hanya.
Legit.ng ta tattaro cewa jami’an hukumar dake kula da afkuwar hadarurruka karkashin jagoranci shugaban yankin Danladi Samari sun kai ziyara gurin don duba gadar da ya rufta.
A halin yanzu, babu rahoto na mutuwa duk da cewan wasu motoci, tankan mai da sauran manyan motoci da suka rufta cikin ramin rusheshen gadar.
Hukumar kula da afkuwar hatsari (FRSC ) Mokwa ne ta saki hotunan gadar na jihar ta shafin sun a Facebook.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli wannan bidiyo na Legit.ng kan yadda yarake kuka da rokon gwamnati da karda ta rushe masu muhalli
Asali: Legit.ng