An buga an barku: Kasimu Yero zai sabunta fim ɗin ‘Magan jari ce’
- Malam Kasimu Yero, ya bayyana cewar babban burinsa a rayuwa
- Kasimu ba burin yin fim din Magana Jari Ce
Shahararren tsohon dan wasan kwaikwayo dake Arewacin Najeriya Malam Kasimu Yero, ya bayyana cewar babban burinsa a rayuwa shine ya mayar da dukkanin litattafan labaran Hausa na Magana Jari Ce wallafar Marigayi Alhaji Abubakar Imam zuwa salon tsari na fim na Zamani domin kara daukaka darajar bahaushe a fadin duniya gaba daya.
Majiyar Legit.ng ta jiyo Dattijo Kasimu Yero ya bayyana hakan ne a lokacin da Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
KU KARANTA: Fasto ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas (Hoto)
Tun dadadewa ne Kasimu Yero ke fama da matsananciyar rashin lafiya kuma yake kwance a gida yana jniya ba tare da samun wata kulawa ta musanman ba, ya cigaba da cewar kullum damuwa da bakin cikin da ke damunshi shine yadda sha'anin harkar finai finai ta tabarbare a Arewa, musamman yadda harkar fina finai a yanzu yayi hannun riga da al'adun Hausawa.
Kasimu Yero ya kuma bayyana cewar tun bayan da wannan lalura ta rashin lafiya ta kwantar dashi shekaru da dama babu wani Jami'in Gwamnati na tarayya ko na Jiha da ya ziyarce shi ballanta har ya samu wani tallafi, sai a wannan rana da Sanata Shehu Sani ya kawo mishi ziyara har gida, inda yayi Addu'ar Allah ya sakawa Sanatan da Alkhairi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Sanata Melaye yan fuskantar matsala
Asali: Legit.ng