June 12: Shin menene muhimmancin wannan rana ga Najeriya?

June 12: Shin menene muhimmancin wannan rana ga Najeriya?

- Janar Babangida ya soke zaben June 12 a 1993

- Ya ta'allaka sokewar kan batun cewa wai wasu manyan kasa basu so

- Wannan ya jawo kusan ballewar kasarnan, kuma ya kawo kashe manyan 'yan siyasar kasar nan

An sake zagayowa ranar june 12, ranar da ke da muhimmanci ga da yawa daga kabilar Yarabawan kasar nan, don ganin a wannan lokaci ne a shekarar 1993 aka hana dan kabilarsu hawa shugabancin kasa, bayan shi ya ci zabe, kuma aka ma kai ga kashe shi, a hannun jami'an mulkin soja.

Matsalar dai a wancan lokacin ta kai ga kusan darewar kasar nan, inda daga baya mai rikon ragamar kasar Cif Ernest Shonekan ya mika wa Janar Sani Abacha mulki, Abachan kuma ya damke Cif MKO Abiola ya wulla a kurkuku, bayan shi Abiolan ya furta cewa shi ne yaci zabe, kuma ya ce shi shugaban Najeriya ne.

An dai yi zabe a lokacin karkashin jam'iyyu da gwamnati ta bari su tsayar da 'yan Takara, SDP da NRC, wadda har kafa gwamnatocin jihohi da majalisu shekaru biyu a karagar mulki. Dan takara Moshood Abiola dan jihar Ogun, ya kayar da bakane Alh. Bashir Usman Tofa har a jihar Kano.

June 12: Shin meye muhimmancin wannan rana ga Kabilar Yarabawa? Dama Najeriya?
June 12: Shin meye muhimmancin wannan rana ga Kabilar Yarabawa? Dama Najeriya?

Kwatsam sai gwamnatin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta ce ta soke zabukan, abun da ya kai ga babban hargitsi da ya yamutsa kasa, har ya kai ga saukar Babangidan daga mulki don tayi masa za kacokan.

An dai mayar wa da kabilar Yarabawa mulki ta hannun shugaba Obasanjo a 1999, bayan rasuwar shugaba abacha, da shugaba Abiola, duk dai a wadannan shekaru na 1998, amma har yanzu ana alhinin rashin adalcin da ya kai ga hana shi Abiola hawa mulki, wanda ake alakanta shi da kin jinin Yarabawa, da kuma son kai na mutanen arewacin Najeriya.

Shugaba Babangida dai bai baiwa jama'a hakuri da wannan kasada ba, amma yace alhakin yana wuyansa, kuma shima ba yadda zayyi ne, wadanda basu son Abiolan ya hau karagar mulki wai sunfi karfinsa, a cewarsa.

Cikin sunayen da aka fi ji ya kama dai a irin wannan rana ta June 12 akwai sarkin Musulmi Dasuki na wancan lokacin, sai marigayi Janar Sani Abacha, sai kuma David Mark, wanda a wata majiyar har alkawarin bindige Abiolan yayi muddin aka ce shine shugaban Najeriya.

Shekarun baya, an saba gudanar da bikin ranar dimokuradiya a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara gabanin shugaba Buhari ya sauya ranar a shekarar 2018.

Buhari ya yi hakan ne domin karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar ta GCFR, domin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel