Korar Inyamurai: Manjo Almustapha zai gana da matasan Arewa

Korar Inyamurai: Manjo Almustapha zai gana da matasan Arewa

Rahotanni sun bayyana cewa, Manjo Al’mustapha wanda shine tsohon babban jami’in mai tsaron lafiyar marigayi shugaba Janar Sani Abacha zai yi wata muhimmiyar ganawa da kungiyoyin matasan arewa don ganin an zauna lafiya tsakanin al’ummar Arewa da‘yan kabilar Igbo.

A jihar Kaduna ne za a gudanar da wannan taro wanda za ta kunshi fahimtar juna tsakanin yankunan biyu bisa dagewa da masu rajin kafa kasar Biafra keyi da kuma wa’adin sallamar ‘yan kabilar Igbo daga Arewa da wasu kungiyoyi suka bayar.

Legit.ng ta samu labarin cewa Manjo Al’mustafa a yayin tattaunawa da manema labarai, yace fahimtar juna ta zame wajibi, domin akwai sa bakin wasu, wadanda basu son zaman lafiya a cikin lamarin, wanda idan anyi sake hakan ka iya haifar da fitina.

Korar Inyamurai: Manjo Almustapha zai gana da matasan Arewa
Korar Inyamurai: Manjo Almustapha zai gana da matasan Arewa

Manjo Al’mustafa wanda ya bada misali da yadda fitina ta gallabi kasar Libya da Sham da Yaman, yace Nijeriya ta gaji da fitina tun yakin basasa Kuma gashi yanzu da kyar aka samu rage kaifin boko haram inji manjon.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng