Shekara 19 da rasuwa: Janar Abacha, ‘sai bayan baka ake’
- Tsohon shugaban kasa a mulkin Soja janar Sani Abacha ya cika shekaru 19
- Tsohon shugaban kasa Abacha ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yunin 1998
A yau 8 ga wata Yuni ne tsohon shugaban kasa a mulkin Soja janar Sani Abacha ya cika shekaru 19 cif cif da rasuwa.
Tsohon shugaban kasa Abacha ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yunin 1998, bayan kwashe shekrau biyar yana mulkin kasar Najeriya daga shekarar 1993.
KU KARANTA: Saudiya ta baiwa Najeriya kyautan kilo 181,437 na dabino
An haifi Abacha ne a ranar 20 ga watan Satumbar 1943 a garin Kano, kuma ya halarci makarantar horar da hafsan Soji dake Aldershot, kasar Ingila, an tabbatar da shi a matsayin cikakken hafsan soji a shekarar 1963.
Janar Abacha yayi kaurin suna a tsakanin abokan aikinsa na Soja wajen tsarawa da shirya juyin mulki, tun yana karamin hafsan soji ya sa hannu a juyin mulkin shekrar 1966 da aka yi don rama kisan Sardauna , Tafawa Balewa da sauran manyan Arewa.
Haka zalika yana daya daga cikin jigajigan Sojojin da suka juya gwamnatin mulkin shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983, wanda yayi sanadiyyar zama Janar Buhari shugaban kasa. Bugu da kari Abacha ne kan gaba wajen juya gwamnatin Buhari, daga nan IBB ya zama shugaban kasa.
A shekrar 1993, 17 ga watan Nuwamba ne Abacha ta ture gwamnatin rikon kwarya na Cif Eranest Shonekan, daga nan ya zama shugaban kasa mai cikakken iko.
A ranar 8 ga watan Yuni Abacha ne ya rasu a kan karagar mulki, kum aka binne shi a jihar Kano. Allah ya jikan sa.
Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin hotunan marigayin don tunawa da shi:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ya za'a idan matarka tafi ka albashi?
Asali: Legit.ng