Kungiyar Bakandamiya na kwace wayoyin salula a hannun 'yan mata

Kungiyar Bakandamiya na kwace wayoyin salula a hannun 'yan mata

- Wani kungiya a kasar kamaru ta fitar da wasu matakai domin dawo da tarbiyyar 'ya'ya mata

- Kungiyar ta dauki matakan kwace wayar salula a hannu duk wata burduwa, da hana su zuwa kasuwanni

- Shugaban kungiyar ya ce 'ya'ya mata ba bi al'adu wadanda ba irin na Hausawa ne ba

- Shugaban ya ce masu neman aure su gabatar da kansu a gidan iyayen yarinya kafin a basu izinin ganawa da su

Kungiyar Bakandamiya reshen garin Touroua ta fitar da wasu matakai domin dawo da tarbiyyar 'ya'ya mata.

A cikin matakan da kungiyar ke dauka, akwai na karbe wa duk wata burduwa wayar hannu, da hana su zuwa kasuwanni.

Wannan matakin ya zo ne a lokacin da daukacin matasa ke cin gajiyar yin amfani da wayar hannu masamman ma ta shafukan sada zumunci.

Kungiyar Bakandamiya na kwace wayoyin salula a hannun 'yan mata
Yara mata reshen garin Touroua da ke kasar Kamaru

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Ishaka Alhadji Manou shi ne shugaban kungiyar Bakandamiya reshen garin Touroua dake arewacin kasar Kamaru. Ya ce sun dauki wannan mataki ne domin ladabatar da matasa masamman ma yara mata wadanda tarbiyyarsu ke tabarbarewa a yanzu haka sakamakon aron al'adun da suke wadanda sun zame baki ga bahaushe da kuma musulmi.

Manou ya ce: "Mun dauki matakai saboda yaranmu mun ga suna lalacewa, suna al'adu wadanda ba irin na Hausawa ne ba. Sai ka ga yarinya ta rike waya irin ta hannu guda 3 ita kadai."

KU KARANTA: Atiku ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Kungiyar ta koka da yadda matasa ke kwaikwayon al'adun da ba nasu ne ba, kuma ta sha alwashin canza lamarin.

A cikin matakan akwai hana dukkan budurwa ko bazawara zuwa kasuwannin kauye, da tabbatar da masu neman aure suna gabatar da kansu a gidan iyayen yarinya kafin a basu izinin ganawa da ita.

Shugaban kungiyar ta Bakandamiya ya kara da cewa, "Har ila yau, mai son yarinya da aure yazo gidan ubanta."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel