Matsafa na farautan masu sanƙo wurjanjan a kasar Mozambique

Matsafa na farautan masu sanƙo wurjanjan a kasar Mozambique

- Yansandan ƙasar Mozambique ta gargaɗi mutane masu sanƙo da Zabiya

- Matsafa sun wasa wukarsu akan masu sanko domin yin tsafin arziki

Hukumar Yansandan ƙasar Mozambique ta gargaɗi mutane masu sanƙo cewa matsafa masu yankan kai na nemansu ruwa a jallo, sakamakon kisan wasu mutane biyar a yan kwanan nan da nufin cire sassan jikinsu.

Sai dai majiyar Legit.ng ta shaida cewar an kama mutum biyu da ake zargi da kisan a tsakiyar lardin Milange, mutanen da aka kama matasa ne guda biyu 'yan kimanin shekara 20.

KU KARANTA: Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

Kamar yadda Kwamandan Yansandan lardin Zambezia Afonso Dias ya bayyana: "Sun yi imani cewa akwai zinare a cikin kan mutumin da ke da sanƙo."

Matsafa na farautan masu sanƙo wurjanjan a kasar Mozambique
Kan mai sanƙo

A shekarun baya ma haka aka dinga kakkashe zabiya a yankin don yin tsafi da sassan jikinsu, don ko a makon jiya sai da aka kashe mutane uku, zabiya.

Matsafan na farautan masu sanko kan cewa sun tsammanin akwai tarin arzikin zinare a cikin kan masu sanƙo, kamar yadda bokaye suka fada musu.

Jami’i Afonso Dias na cewa "manufarsu ba ta rasa nasaba da camfi da al'adar mutanen yankin da ke zaton mutanen da ke da sanƙo zasu yi arziki."

Shima kaakakin rundunar tsaro yace waɗanda ake zargin sun ce ana amfani da sassan jikin ne wajen yin asiri don samun ƙaruwar arziƙi ga masu kuɗin da ke zuwa neman magani daga Tanzania da Malawi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abin mamaki, makafi gida 4:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng