'Zan fasa kwai kan kisan Abiola' - Hamza Al-Mustapha

'Zan fasa kwai kan kisan Abiola' - Hamza Al-Mustapha

- Tsohon mai kula da tsaron marigayi Janar Abacha ya dawo idon jama'a da sabon batu da aka dade ana jira

- Al- Mustapha yasha dauri kan zarginsa da kashe Mrs. Kudirat Abiola, matar MKO Abiola

- Yace a kan wani faifan bidiyo ne kadai aka kama shi, anyi-anyi ya bayar a kona yaki

Tsohon Mai kiyaye tsaron lafiyar tsohon shugaban soja Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, wanda yasha dauri tun daga 1998 har zuwa 2013 yace an rufe shi ne ba a kan komi ba sai wani faifan bidiyo da kyamarar cikin Aso Rock Villa ta kama ana kitsa yadda a'a kashe Abiola.

"Ita kyamarar boyayyiya ce, kuma shi ya saka ta, ta kuma kama fuskokin wadanda suka kitsa shirin, kuma ya dauke bidiyo kaset din ya boye, amma akayi akayi ya bayar dashi yaki, sai ko aka kama shi aka kala masa kisan Alhaja Kudirat Abiola", a cewarsa.

'Zan fasa kwai kan kisan Abiola' - Hamza Al-Mustapha
'Zan fasa kwai kan kisan Abiola' - Hamza Al-Mustapha
Asali: Facebook

Yana wannan bayanin ne a jihar Oyo, a wani taro da yake halarta na kara wa samari kwarin gwiwar shiga harkar siyasa.Yace an kulle ni a makuntacin hali, an yi ta yawo dani gidajen yari a Lagos, amma ban karaya ba.

KU KARANTA KUMA: 'Namadi Sambo ya san da alaka ta da Boko Haram' - Sanata Ndume

Yace littafinsa nan fitowa guda uku, wanda zayyi bayanan sirri dalla dalla ciki harda batun Abiola. Ya kuma musanta cewa shi ya saka aka kashe Matar Abiolan, inda yace shi makusancin iyalin Abiola ne, ba zai cuce su ba.

Ya kuma alamta wani daga cikin masu hannu a kisan Abiolan da cewa dayansu yanzu baya iya tafiya sai da gudummawa.

Abin tsoron dai a nan shine, in dai da gaske ne batun da yake fada, kuma jiga-jigan da zai tabo suna da karfi, zasu barshi yayi rai har ya iyar da nufinsa? Ko kuma zasu sake masa bita-da kulli?

Asali: Legit.ng

Online view pixel