Kasashen Larabawa 4 da suka yanke alaka da Qatar

Kasashen Larabawa 4 da suka yanke alaka da Qatar

Kasashen Saudiyya, Bahrain, Masar da Daular Larabawa wacce akafi sani da Dubai sun sanar da yanke huldar diflomasiya da kasar Qatar zargin daukan nauyin ta’addancin da akeyiwa kasar Qatar.

Tashar yada labaran kasar Saudiya ta bada rahoton cewa bayan katse huldar diflomasiyar, kasar ta kuma rufe iyakokinta da Qatar kana bin da ta kira kare kare kanta daga hare haren ta’addanci.

Ita kuma kasar Masar ta ce bayan daukar wannan matakin, za ta rufe tasoshin jiragen sama da na ruwa zuwa Qatar.

Kasar Bahrain kuma, ta zargi Qatar da haifar da matsalan tsaro a cikin kasarta tare da shiga sha’anin harakokin cikin gidanta.

Kasashen Larabawa 4 da suka yanke alaka da Qatar
Kasashen Larabawa 4 da suka yanke alaka da Qatar

Kasashen kuma sun kori Qatar daga cikin kungiyar kawancen kasashen larabawa da Saudiya ke jagoranta wajen yakar ‘yan tawayen Yemen.

Kasashen sun zargi Qatar da taimakawa kungiyoyin ta’adda da suka hada da al Qaeda da kungiyar ISIS.

KU KARANTA: NUPENG tace sam ba zata yarda da karin kudin man fetur ba

A kwanakin baya ne kasar Amurka ta saki jawabi da ku nuna cewa kasar Qatar na taimakawa yan tawaye da yan ta’ddan duniya. Ga dukkan alamu, kasashen larabawa sun amince da wannan bincike na kasar Amurka.

Kasar Qatar ta musanta zargin da ake mata na daukar nauyin ta’addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng