Wata jaririya ta sanya mutane cikin ruɗani bayan ta aikata wani abin al’ajabi

Wata jaririya ta sanya mutane cikin ruɗani bayan ta aikata wani abin al’ajabi

- Tinkis! Tinkis!! taken tafiyar wata jaririya kenan

- Jaririya ta baiwa mutane mamaki a kasar Brazil bayan tayi tattaki da kafarta

Wata Jaririya ta baiwa mutane mamaki a kasar Brazil bayan tayi tattaki da kafarta jim kada da haihuwarta, inji rahoton jaridar Mirror UK.

Jaririyar tayi wannan abin ban mamaki ne yayin da likitocin asibitin da aka haife ta ke kokarin yi mata wanka, kwatsam sai aka ganta tat a fizge daga hannunsu tana taka taka.

KU KARANTA: Ramadan: Ribadu da Magu zasu tattauna muhimmancin yaƙi da rashawa a watan

Ba kasafai aka saba ganin haka a duniya ba, saboda a tsarin halitta, jarirai basa fara tafiya sai sun kai watanni 12, wannan lamari ya faru ne a babban asibitin Santa Cruz dake garin Rio Grande do Sul, Kudancin Brazil.

Wata jaririya ta sanya mutane cikin ruɗani bayan ta aikata wani abin al’ajabi
Jaririya

Wata shaidan gani da ido ta bayyana ma Majiyar Legit.ng “Jaririyar ta bani mamaki matuka, idan kasance a haka, ba’a san me zata kasance idan garinta ba.”

Ita ma unguwar zomar data amshi haihuwar tace “Abin mamaki, idan ka fada ma jama’a abinda ya faru ba zasu yarda ba, har sai mutum ya gani da idanunsa.”

Amma ita kam matar tace bata ji mamakin hakan ba, inda tace akan samu hakan, sai dai ba sosai ba.

Wannan tsarin tafiyar, yana kasancewa ne kamar “Da aka rike jarirai ta kasar hammata, sai aka sakan mata kafa a kasa, ana yin hakan, sai kawai yarinyar ta fara takawa tinkis, tinkis.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya auran kabila?

Asali: Legit.ng

Online view pixel