Alhamdulillah: Musulunci ya samu ƙaruwa
- Wani matashin kirista ne ya musulunta a jihar Sakkwato
- Matashin ya musulunta ne bayan ya halarci taron wa’azin Tafsiri a wani Masallaci
Gaskiya ne, duk wanda Allah yayi ma shiriya, toh ba zai taba bacewa ba, wannan shine kwatankwacin abin daya wakana a ranar Alhamis 1 ga watan Yunin 2017, kamar yadda Rariya ta samu rahoto.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani matashin kirista ne ya musulunta a jihar Sakkwato bayan ya halarci taron wa’azin Tafsiri a wani Masallaci dake Unguwar Koko cikin birnin Sakkwato.
KU KARANTA: Gwamnati ta samar da dokoki guda 9 da zasu taƙaita zuƙan sigari (KARANTA)
Limamin wannan Masallaci na Ali Bn Abi Talib, Malam Bashar Ahmad Sani ne ya baiwa wannan matashi kalmar shahada, inda nan take ya musulunta kuma ya sauya suna.
Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, bamu tabbatar da tsohon sunansa ba da kuma sunan daya canza.
Dama dai ana yawan samun jama’a wadanda ba Musulmai ba suna karbar addinin Musulunci, musamman a watan Azumi yayin da ake gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani mai girma, don ko a Azumin bara an samu sabbin Musulmai da dama maza da mata a masallatai daban daban.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Batutuwan aure, kalla
Asali: Legit.ng